Kotu zata saurari karar yunkurin cire shugaban EFCC

Kotu zata saurari karar yunkurin cire shugaban EFCC

- Za a saurari karar cire Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC a watan Oktoba

- Johnmary Jideobi ya shigar da kara inda ya ke neman kotu ta dakatar da Magu a matsayin shugaban EFCC

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kalu balanci yunkurin cire Magu

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta ce zata fara saurari karar yunkurin cire shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, Mista Ibrahim Magu a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa. Wani lauya Johnmary Jideobi ya shigar da kara inda ya ke neman a cire Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar Jideobi yana nema kotun ta yi bayanin dakatar da Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC.

KU KARANTA: Shure-shuren mutuwa kungiyar Boko Haram ke yi – Buratai

Kotu zata saurari karar yunkurin cire shugaban EFCC

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, Mista Ibrahim Magu

Ya ce majalisar dattijai ta ki amince da shi bayan da shugaban kasa ya mika sunansa ga ‘yan majalisdar don a tantance shi kuma a bisa doka wa’adin zaman sa shugaban hukumar ta zo karshe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel