Mutane 4 da su ka yi kaca-kaca da Fayose game da rashin lafiyar Buhari

Mutane 4 da su ka yi kaca-kaca da Fayose game da rashin lafiyar Buhari

– Gwamnan Imo Okorocha ya karyata Fayose game da batun ciwon Buhari

– Haka kuma Jam’iyyar APC ta ce Ayo Fayose ya fito da hujjojin sa

– Wata Kungiya ta magoya bayan Buhari ba ta kyale Gwamnan haka ba

Mista Ayo Fayose Gwanan Ekiti yace Shugaba Buhari ko numfashi ba ya iya yi, wanda hakan ya sa Jama’a da dama su ka dura kan sa, wanda har ‘Yan Jam’iyyar adawa ba su raga masa ba. Ga dai kadan daga cikin su:

Mutane 4 da su ka yi kaca-kaca da Fayose game da rashin lafiyar Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da lafiya

1. Gwamna Rochas Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha wanda shi ne shugaban Gwamnonin APC ya karyata wannan magana ta Fayose dazu a Abuja.

KU KARANTA: Inyamurai su na cikin amana a Kano Inji Gwamna

Mutane 4 da su ka yi kaca-kaca da Fayose game da rashin lafiyar Buhari

Rashin lafiyar Buhari: Ashe Ayo Fayose karya yake yi?

2. Sanata Buruji Kashamu

Duk da cewa Sanatan ‘Dan Jam’iyyar PDP ne amma ya karyata Gwamnan na Jihar Ekiti da yace kusan makonni uku kenan Buhari bai san inda yake ba.

3. Jam’iyyar APC

Tuni dai Jam’iyyar APC mai mulki ta karyata Gwamnan na Ekiti. Jam’iyyar ta nemi Fayose yayi baja-kolin dalilai idan ba karya yake yi ba

4. BMSG

Kungiyar ‘Buhari Media Support Group’ watau masoya Buhari da ke kan kafafen yada labarai sun ce dai dama ba yau Gwamnan ya fara sheka karya ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gobara ta tashi a Abuja [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel