Najeriya ba zata cigaba ba har sai an samu saukin tashe-tashen hankula - Wamakko

Najeriya ba zata cigaba ba har sai an samu saukin tashe-tashen hankula - Wamakko

- Aliyu Wamakko ya bayyana cewa kasar Najeriya bazata taba samun cigaba ba har sai an daina yawan rikici

- Ya ce babu kasar da za ta cigaba a cikin rashin tsaro, rigima, sabani, rikice-rikice, da tashin hankula

- Wamakko ya yaba ma mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Sanata mai wakiltar arewacin jihar Sokoto, Aliyu Wamakko ya bayyana cewa kasar Najeriya bazata taba samun cigaba ba har sai an daina yawan rikici da tashe-tashen hankula da ke afkuwa a yau da kullum tsakanin yankuna da kabilun a Najeriya.

Ya ce babu kasar da za ta cigaba a cikin rashin tsaro, rigima, sabani, rikice-rikice, da tashin hankula kuma babu wani girmamawa da yabo ga kasar da ta chude a cikin hatsaniya.

Wamakko ya kara da yabawa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, kan kokarinsa na inganta tsaro da tabbatar da haddin kan kasa.

KU KARANTA KUMA: Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo

Najeriya ba zata cigaba ba har sai an samu saukin tashe-tashen hankula - Wamakko

Najeriya ba zata cigaba ba har sai an samu saukin tashe-tashen hankula cewar Wamakko

A wani al’amari makamancin wannan NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da cewa babu inda ‘yan kabilar Igbo mazauna jihar za su.

Ya fadi hakan ne a kan wa’adin barin gari da wasu kungiyoyin matasan Arewa suka ba ‘yan kabilar Igbo.

Gwamnan ya fadi hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu kawo rahoto a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja, a ranar Laraba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel