Ina masu motoci? Hamid Ali yayi bayani kan hanyoyin tantance takardun mota na bogi

Ina masu motoci? Hamid Ali yayi bayani kan hanyoyin tantance takardun mota na bogi

Shugaban hukumar yaki da fasa kauri, Hamid Ali ya bayyana wani sabon hanya da za’a iya bi wajen tantance ingancin takardun mota don gane na bogi da kuma sahihi.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Hamid Ali yana fadin hukumar tasa ta kaddamar da wasu sabbin lambobi da za’a iya amfani dasu wajen gani sahihancin takardun mota.

KU KARANTA: 2019: Kwankwasawan jihar Katsina sun yi kira da babban murya ga Sanata Kwankwaso

“Zaka iya kiran wannan lambar: 094621597, ko kuma ka aika sakon waya zuwa ga lambar, sakon naka ya kasance ya kunshi C-lamba na mota, shekarar da ka biya mata duti da kuma sunan tashar da jirgin ruwan ta shigo zuwa Najeriya.

Ina masu motoci? Hamid Ali yayi bayani kan hanyoyin tantance takardun mota na bogi

Hamid Ali

“Da zarar an aika da wannan, a cikin mintunan biyar za’a samu amsa daga hukumar kwastam da zai tabbatar sahihancin takardun motar ko kuma akasin haka.” Inji Hamid Ali.

Ina masu motoci? Hamid Ali yayi bayani kan hanyoyin tantance takardun mota na bogi

Motoci

Ali ya kara da cewa za’a iya canza lambar karshe daga cikin lambobin, wato 7, zuwa lamba 8 ko 9 domin samun amsa da gaggawa. Sa’annan yace an yi hakan ne don sawwaka ma dilolin motoci gane sahihancin takardunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo muku bidiyon Najeriya kasa daya, al'umma daya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel