Kiristoci sun yi wani kira ga Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

Kiristoci sun yi wani kira ga Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

– ‘Yan Darikar Angilika sun nemi a bayyana nawa abin da EFCC ta samu

– Haka kuma mabiya addinin Kiristan sun nemi a daina kawo rikici a kasar

– Ku na da labari cewa an nemi Shugaban kasa Buhari yayi murabus

Wani babban Cocin Angilikan ya nemi a fadawa Najeriya abin da EFCC ta samu. An kuma nemi a daina kokarin tada zaune-tsaye a Arewaci da Kudancin kasar. Kwanan nan dai aka yi wannan kira wurin Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo.

Kiristoci sun yi wani kira ga Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

‘Yan Darikar Angilika sun nemi a bayyana abin da EFCC ta samu

Mabiya addinin Kirista na Darikar Angilikan da ke Jihar Enugu sun nemi Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana ainihin kudin da Hukumar EFCC ta samu kwanaki a wani gida a Ikoyi domin Jama’a su samu yakinin cewa da gaske ake yakar sata.

KU KARANTA: Tsirarun 'Yan Boko Haram ne su ka rage

Kiristoci sun yi wani kira ga Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

Shugaba Buhari ya sauka daga kujera Inji Cocin Angilikan

Babban Cocin Angilikan din ya kuma nemi a daina kawo abin da zai tada rikici a Najeriya a wannan lokaci da ake kokarin korar Inyamuran da ke Yankin Arewa. Mabiyan sun yi gargadin cewa shigen haka ne dai ya kawo Yakin Biyafara.

Kun ji cewa Babban Cocin Angilikan da ke Jihar Enugu yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus ganin yadda rashin lafiya ta tasa shi a gaba. Mabiyan cocin dai sun yi wa Shugaban kasar addu’ar samun waraka.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel