Kamaru ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 887 zuwa gida

Kamaru ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 887 zuwa gida

- An dawo da ‘yan gudun hijira 887 daga kasar Kamaru zuwa Najeriya da amincewarsu

- Kamaru da Najeriya sun kula yarjejeniya kan yadda za a dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa garuruwansu a watannin baya

- Ana zargin Kamaru da keta yarjejeniyar Yaounde da aka amince wajen dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa Najeriya

Kasar Kamaru ta dawo da ‘yan Najeriya da suka tsere wa rikicin Boko Haram su 887 zuwa garin Banki, wanda ke iyakar kasashen biyu a wani mataki da aka ruwaito cewa wannan mataki nada amincewar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, watannin baya bayan nan ne dai aka kulla wata yarjejeniya kan yadda za a dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa gida, amma da amincewarsu, yarjejeniyar da aka kulla karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Honarabul Muhammad Sani Zoro, shugaban kwamitin kula da matsalolin yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram, ya ce akwai dalilai biyu dangane da dawowar ‘yan gudun hijirar zuwa gida.

Kamaru ta dawo da wasu ‘yan Najeriya 887 zuwa gida

‘Yan gudun hijirar da aka dawo da su daga Kamaru zuwa gida

A cewarsa Kamaru ta dade tana keta yarjejeniyar Yaounde da aka amince wajen dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa Najeriya duk da cewa alhakin kula da su ya rataya a kan wuyanta a matsayinsu na ‘yan gudun hijira.

KU KARANTA: An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

Sannan ‘yan gudun hijirar na amincewa ne su dawo saboda an samar da tsaro a garuruwansu daga barazanar Boko Haram.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel