Shugaba mai rikon kwarya, Yemi Osinbajo yayi sabbin nade-nade har 14

Shugaba mai rikon kwarya, Yemi Osinbajo yayi sabbin nade-nade har 14

- Shugaban kasa mai rikon kwarya Yemi Osinbanjo yayi na’am da nadin shugabanin hukumomin lafiya ta kasa.

- Wadanda aka nada zasuyi aiki ne a matsayin direktocin a asibitocin koyarwa da asibitocin kwararu dadan-daban a Najeriya.

- Ministan lafiya Isaac Adewole, da wasu mutane biyar wanda aka nada zasuyi aikin karo na biyu wanda kuma shine na karshe.

Shugaban kasa mai rikon kwarya Yemi Osinbanjo ya sa hannu a takardan da tayi na’am da nadin mutum 14 a matsayin manyan direktoci na lafiya, da kuma direktocin lafiya a asibitocin kwararu, da kuma asibitocin koyarwa ta tarayya.

A cikin wasikar da ke dauke da sa hannun mukadashin mai taimaka wa shugaban kasan mai rikon kwarya, wanda aka aika wa minsitan lafiya Isaac Adewole, mutane biyar daga cikin wanda akayi nadin zasu aiki ne karo na biyu kuma na karshe.

Bayan ya taya wandanda aka nada murna, Ministan Lafiyan ya kiraye su da su dukufa wajen aiki babu kama hannun yaro.

Shugaba mai rikon kwarya, Yemi Osinbajo yayi sabbin nade-nade har 14

Shugaba mai rikon kwarya, Yemi Osinbajo yayi sabbin nade-nade har 14

Adewale ya cigaba da cewa yana wandanda aka nada zasu bada gudunmwar su wajen samar da ingantanciyar lafiya bisa ga tsarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na samar da lafiya a kasa baki daya.

Sunayen wadanda aka nada a matsayin manyan masu gudanar da ma’aikatun lafiya sun hada da:

1. Bisala Ekele

2. V.A Osiatuma

3. Idris Suleiman

4. Abdus Musa

5. O.O Alabi

6. Adejuwon Dada

7. Ibrahim Wakama

8. O.C Ogun

9. Shehu Sale

Mutane biyar din da suyi aikin nasu na karshe sune:

1. A.Z. Mohammed

2. Anthony Igwegbe

3. Wiza Inusa

4. Joseph Okegbe

5. Sunday Olotu

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel