Shure-shuren mutuwa kungiyar Boko Haram ke yi – Buratai

Shure-shuren mutuwa kungiyar Boko Haram ke yi – Buratai

- Shugaban hafsan soji Tukur Buratai ya kalubalanci kungiyar Boko Haaram

- Ya ce duk wani hari da suke kai wa a yanzu shure-shure ne kafin mutuwa

- Buratai ya ce sun rigada sunyi nasara a kan su

- Daga karshe ya bukaci ýan fararen hula da su bayar da tasu gudunmawar gurin inganta tsaro

Duk da ci gaba da kai hare-hare da kungiyar ýan taáddan Boko Haram ke yi a jihar Borno da ma wasu sassa na yankin arewa maso gabashin kasar, shugaban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya tabbatarwa ‘yan Najeriya da cewan sun gama da kungiyar kuma hare-haren da ta ke kaiwa ba wani abu bane illa shure-shuren mutuwa.

Buratai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a taron bunkasa tsaron kasa da makarantar koyan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya ta shirya a jihar Lagas.

Ya kara da cewa sun kafa gidajen rediyo a gurare masu muhimanci domin ilimantar da mabiya kungiyar Boko Haram gaskiyar koyarwar addinin Islama.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta haifi kadangare a Port Harcourt (hotuna)

Shure-shuren mutuwa kungiyar Boko Haram ke yi – Buratai

Shure-shuren mutuwa kungiyar Boko Haram ke yi cewar Tukur Buratai

Ya ci gaba da cewa, suna ganin nasarori sosai a kokarin da suke yi, kuma duk wani abu da kungiyar Boko Haram za ta yi a yanzu ba wani ab bane illa shure-shuren dab da mutuwa.

Buratai wanda daraktan kula da hulda da jama’a na rundunar sojin Birgediya Rabe Abubakar ya wakilta, ya bayyana muhimmancin hada hannu da fararen hula daga kowane bangare da sako na Najeriya domin tabbatar da an samu zaman lafiya.

A cewar shi: “zamanin da ‘yan Najeriya ke jin tsoron sojoji ya wuce, dukkan mu ‘yan Najeriya ne kuma kowannen mu na da muhimmanci a yakin da ake yi da ta’addanci.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel