An yi jana’izar sojoji biyu da suka rasu sakamakon harin Boko Haram a Borno

An yi jana’izar sojoji biyu da suka rasu sakamakon harin Boko Haram a Borno

- An yi jana’izar sojoji biyu da suka riga mu gidan gaskiya a Gombe

- A binne sojojin ne bisa addini musulunci a makabarta sojoji da ke Gombe

- Dakarun soja Najeriya sun cire turmi bomb da kuma gano wasu harsasai daga ‘yan Boko Haram

An yi jana'izar sojojin Nijeriya guda biyu da suka rasu a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni da ta gabata a hanyar Damboa-Biu dake jihar Borno sakamakon harin Boko Haram.

An binne Lance Corporal Auwal Halliru da Private Halilu Aliyu na bataliya 254 Task Force bisa addini musulunci a makabarta sojoji da ke Gombe.

KU KARANTA: Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

An yi jana’izar sojoji biyu da suka rasu sakamakon harin Boko Haram a Borno

Sojoji biyu da suka rasu sakamakon harin Boko Haram a Borno

NAIJ.com ta ruwaito cewa, a wata sintirin dakarun bataliya 151 na 21 Brigade a kauyen Mayanti a ranar Laraba, 28 ga wata Yuni 2017, dai dai da karfe 3.30 na dare, inda kungiyar Boko Haram suka kai wa sojojin hari, amma dakarun sun ci galaba akansu. Dakarun sun cire turmi bomb da kuma gano wasu harsasai daga ‘yan ta’addan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel