Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Mista Barack Hussain Obama, tsohon shugaban kasar Amurka tare da iyalinsa sun isa kasar Indonesiya don hutawa da kuma yawon bude ido, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Barrack Obama tare da uwargidarsa Michelle da kuma yayansu guda 2, Sasha da Malia sun fara sauka ne a masaukinsu dake Bali, inda a ranar Laraba 28 ga watan Yuni suka kai ziyara dakin bauta na Budda dake garin Java.

KU KARANTA:An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

NAIJ.com ta tattaro bayanai cewar kasar Indonesiya ba bakuwar kasa bace a wajen Obama, inda ko a bayan rasuwar mahaifinsa, uwarsa ta sake auran wani dan kasar Indonesiya, wanda shi ya rike Obama har girmansa.

Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Obama da yarsa

Ana sa ran a ranar Juma’a 30 ga watan Yuni ne shugaba Obama zai tattauna da shugaban kasa Indonesiya Joko Widodo a fadar gwamnati dake babban birnin kasar, Jakarta.

Ga sauran hotunan nan:

Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Obama

Obama da iyalinsa

Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Jama'a na gaishe su

Anyi ma Barack Obama babban tarba a ƙasar Indonesiya inda yaje yawon hutu (HOTUNA)

Yayan Obama

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zafafan labaru:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

NAIJ.com
Mailfire view pixel