Miji da mata sun taka sawun ɓarawo: An kama su da wayar wata mata da aka yi garkuwa da ita, kuma aka kashe ta

Miji da mata sun taka sawun ɓarawo: An kama su da wayar wata mata da aka yi garkuwa da ita, kuma aka kashe ta

- Wasu ma'aurata sun shiga komar yansanda bayan taka sawun barawo

- An kama su ne da wayar salular wata mata da aka hallaka

NAIJ.com ta samo wani rahoto dake nuna cewar wasu ma’aurata yan Najeriya sun shiga tsaka mai wuya bayan da aka kama su dauke da wayar salular wata mata da aka kashe a kwanakin baya.

Ma’auratan masu suna Emeka da Monica sun shiga hannun yansanda ne bayan da aka kama wayar wata mata da aka kashe mai suna Amaka Okere a hannunsu, matar da aka sace ta don yin garkuwa da ita, daga bisani kuma ak tsinci gawar ta a unguwar Mbieri na jihar Imo.

KU KARANTA: Da alama jami’an tsaro ba zasu iya maganin masu aikata miyagun laifuka a jihar Neja ba - Gwamna

Maigida Emeka yace matar ce ta bashi wayar a matsayin kyauta: “Na rantse, ban san komai game da wayar nan ba, mata tace ta bani shi, kwatsam kuma sai Yansanda suka kama ni, wayar nan ta sanya ni cikin jafa’i.”

Miji da mata sun taka sawun ɓarawo: An kama su da wayar wata mata da aka yi garkuwa da ita, kuma aka kashe ta

Ma'auratan

Ita ma uwargida Monica cewa tayi kanwarta ce ta bata wayar, kamar yadda ta shaida ma jaridar Vanguard, inda tace ita yar asalin jihar Abia ce, kuma ta ziyarci kanwarta ne a jihar Akwa Ibom, inda a lokacin da zata tafi ne ta bata kyautar wayar.

Sai dai kwamishinan yansandan jihar Imo, Chris Ezike ya bayyana ma maneman labaru cewar:

“A aranr 1 ga watan Maris ne aka yi garkuwa da Uwargida Amaka Okere mai shekaru 45 a karamar hukumar Mbaitoli, unguwar Mbieri na jihar Imo, daga bisani kuma aka kashe ta. A yanzu dai zamu cigaba da gudanar da bincike akan Monica da Mijinta Emeka.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin za'a iya samun hadin kai a Najeriya kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel