Jirgin Shugaba Buhari ba zaman dirshan yake ba Ingila - Garba Shehu

Jirgin Shugaba Buhari ba zaman dirshan yake ba Ingila - Garba Shehu

- Rashin sanin tsarin dokar kasa yasa wasu mutane ke korafe-korafe akan jirgin Buhari da ke Ingila

- Kudin da ake kasha ma jirgin bai haura fam 1000

- Kowane shugaban kasa yana bukatar jirgin sa saboda tsaro da kuma kare mutunci da kimar kasarsa.

Babban mai taimaka ma shugaban kasa Muhammadu Buhari akan hulda da jama’a Garba Shehu yayi bayani akan shafinsa na facebook akan korafe-korafen da jama’a keyi akan ajiyar jirgi kirar NAF 001 da ke ajiye a birnin London inda shugaban kasan ke samun kulawa na likitoci.

Yace korafe-korafen sun taso ne saboda rashin sanin yadda dokar kasa ta tsara tafiye-tafiyen shugaban kasar. Saboda dalilai na tsaro, kare mutunci da kimar kasa, babu shugaban kasar da zaiyi tafiya ba tare da shirin ko ta kwana ba.

Har illa yau, tunda shugaban kasa ne babban kwamandan dakarun sojojin Najeriya, babu yadda Sojojin saman zasu yadda kwamandan nasu a wani gari su tafi. Wannan haka dokar take a duk kasashen duniya.

Jirgin Shugaba Buhari ba zaman dirshan yake ba Ingila - Garba Shehu

Jirgin Shugaba Buhari ba zaman dirshan yake ba Ingila - Garba Shehu

Mun samu labarin zunzurutun kudin da aka ce ana biya wa jirgin, wannan zancen ba gaskiya bane, jiragen shugabanin kasashe ana masu rahusa na musamman, kuma idan ma ba’a yi rahusar ba an tabbatar mana cewa kudin ajiyar jirgin ba zai haura fam 1000 ba wanda ko kusa bai kai kudin da ake yayatawa ba.

Shugaba Buhari bashi bane shugaban kasa na farko hakan ta faru dashi kuma ba zai zama na karshe ba. Dukan shugabanin Najeriya ta suka shude sun sami wannan gatar, wasu ma har jirage uku suke yawo dasu amma ba’a tsangwame su haka ba.

“Ina kira gay an Najeriya da suyi watsi da wannan maganar domin surkule ne kawai nay an adawa.

“Muna da gwamnati da ke gina gadar niger na biyu, aikin wutan lantarkin mambila, da kuma shjimfida layyukan dogo na zamani a duk fadin kasar nan.” Inji Shehu Garba

Gwamnatin mu tayi maganin ma’aikatan bogi, kuma ceto kudin kasa wanda ya kai tiriliyoyin naira daga hannun masu satan kudin da sunnan tallafin man petur. Ya kamata jama’a suyi ma gwamnatin Buhari uzuri.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel