Kudar zuma ta sa wani barawon mota mika kansa ga ‘Yan Sanda

Kudar zuma ta sa wani barawon mota mika kansa ga ‘Yan Sanda

A ranar Litinin din da ta gabata ne wani barawon mota ya fada ofishin ‘yan sanda a guje tare da mika kansa a matsayin barawo sakamakon kudar zuma da ta mamaye shi da kuma harbinsa.

Wannan al'amari ya afku ne a kasar Kenya, inda wani mutumi dan asalin kasar Uganda mai suna Francis Sikadigu ya yi amfani da kwayoyin da ke fitar da mutum daga hayyacinsa wajen sace shi da motarsa zuwa wani waje inda a nan ne ya sace motar.

Bayan sace motar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sai mai motar ya kai kukansa wajen wani boka, inda boka ya dauki gabarar hukunta barawon tare da sa shi dawo da motar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Bungoma, Mista Kirui ya tabbatar da wannnan labarai inda ya ke cewa “Abinda ya faru ba komai ba ne face maita kiri-kiri”. Za mu mika wanda ake zargi zuwa kotu da zarar mun kammala bincikenmu.

KU KARANTA KUMA: Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Kudar zuma ta sa wani barawon mota mika kansa ga ‘Yan Sanda

Kudar zuma ta sa wani barawon mota mika kansa ga ‘Yan Sanda

Mai motar, Mista John Wafula, wanda sanannen mai hayar motoci ne ya bayyana cewa: “Barawo Sikadigu ya zo wajen don na bashi hayar motata na tsawon kwanaki uku a ranar Juma’ar da ta gabata, muna cikin tattauna farashin ne sai na dan bar wajen, inda a nan ne ya samu dama ya jefa wata kwaya a cikin abin sha na. Kawai farfadowa na yi na ganni a babban asibitin garin Bungoma County.”

Mista Wafula ya ci gaba da cewa: “Bayan na kai rahoto gurin ‘yan sanda, sai na wuce wajen wani boka don a yi min aiki motata ta fito.

“Ina godiya ga ubangiji da ya dawo min da motata kuma aka kama barawon. Ina son hukuma ta gurfanar da shi a gaban kotu don ya zama darasi a gareshi da sauran mutane.”

‘Yan sanda sun nemi Wafula da ya kai su ga bokansa don ya sa kudar zuman da ta yanyame Sikadigu da ta bar jikinsa kuma sun yi nasarar samun boka Siraba Musali da aka fi sani da Dakta Nyuki a rukunin gidaje na Marell, inda bayan ya yi ‘yan kulumbotonsa ne zuma ta bar bin Sikadigu, kuma ‘yan sanda suka koma da shi ofishinsu don ci gaba da bincike

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel