An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

Ta bayyana Shugaban kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fara gajiya da yakin sunkuru da tada kayar baya da kungiyar tasu take yi da gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana iya fahimtar hakan ne a cikin sabon faifan bidiyon da kungiyar ta fitar inda aka nuna Shekau yana jawabi tare da ikirarin wai sun saci manyan jami’an Yansandan Najeriya mata a kusa da garin Maiduguri a ranar 20 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 3 da Shekau ya fada a cikin sabon faifan Bidiyon sa

Sai dai tuni rundunar Yansandan jihar Borno ta musanta wanna batu, inda ta kalubalanci Shekau daya nuna hotunan matan idan da gaske yake, tun da dai dama ai haka ya saba yi.

An ci Boko Haram da yaki? Shekau ya karaya a sabon bidiyon daya fitar

Shekau a sabon bidiyon daya fitar

Wata alama dake nuna Shekau ya fara karaya itace, a bidiyon daya fitar mai jimillar tsawo mintun 16, mintuna 6 kacal yayi yana magana, sauran mintunan kuwa wake wake kawai suka sanya, ba kamar yadda ya saba yi ba a baya inda yake kwashe tsawon mintuna yana surutu.

Bugu da kari ba’a saba ganin Shekau yana magana a hankali cikin natsuwa ba duk fayafayan bidiyon dayake fitarwa a baya ba, amma sai ga shi a wanna bidiyon ya ya natsu tamkar wanda ruwa ya buga.

Daga karshe, a maimakon Boko Haram ta nuna yadda take samun nasara aka Sojojin Najeriya kamar yadda take ikirari, sai gashi tana nuna wasu hotunan sojojin suna harbe harbe, suna harbin iska ba tare da ganin keyar sojan Najeriya ko daya ba.

Kalli bidiyon a nan:

NAIJ.com ta ruwaito wasu masana na bayyana cewar wannan hotunan na mayakan Boko Haram dake harbe harben iska ma tsohon boidiyo ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga zanga zangar yan matan Chibok:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel