Tsirarun yan Boko Haram ne kawai suka rage - Inji Rundunar tsaron Najeriya

Tsirarun yan Boko Haram ne kawai suka rage - Inji Rundunar tsaron Najeriya

- Yan tsirarun yan ta'addan Boko Haram ne kawai suka rage yanzu

- Jami'an rundunar tsaron Najeriya ne suka bayyana hakan

- Masana da dama ma dai sun bayyana cewa an ci lagon yan ta'addan

Rundunar tsaron Najeriya tace burbudin ‘yan Boko Haram ne da suka rage, suke kai ‘yan hare haren da ake gani a baya bayan nan.

Da yake jawabi ga manema labarai, darektan watsa labarai na rundunar Majo Janar John Enanche, ya bayyana cewa, suma ba wata babbar barazana bace, ya kuma bada tabbacin cewa, suma nan ba da dadewa ba za a shawo kansu.

Tsirarun yan Boko Haram ne kawai suka rage - Inji Rundunar tsaron Najeriya

Tsirarun yan Boko Haram ne kawai suka rage - Inji Rundunar tsaron Najeriya

NAIJ.com ta samu labarin cewa tun bayan kwace jejin Sambisa aka daina jin dakarun kasar suna kai hari kan kungiyar Boko Haram, amma a maimakon haka, sai kungiyar take kara zafafa kai hare hare.

Tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Kano, majo janar Idris Garba mai ritaya wanda ya kasance masanin tsaro ya bayyana cewa, kungiyar bata da karfi yanzu sabili da an warwatsar da membobinta gaba daya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel