Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo

Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo

- Gwamna Ganduje ya kaddamar da cewa babu inda ‘yan kabilar Igbo mazauna jihar za su

- Ya ce Kano gidan kowa ne ba bako ba dan gari

- Ya kara da cewa zasu nuna misali bai bam mamaki

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da cewa babu inda ‘yan kabilar Igbo mazauna jihar za su.

Ya fadi hakan ne a kan wa’adin barin gari da wasu kungiyoyin matasan Arewa suka ba ‘yan kabilar Igbo.

Gwamnan ya fadi hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu kawo rahoto a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a Abuja, a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo

Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo

Ganduje ya yi ammana da cewa kowa dake zaune a Kano dan asalin jihar ne.

Ya bayyana cewa gwamnatin sa bata ware dan kansa ko wanda ya zo zama a gurin kula da al’amuran jihar don haka kuma ‘yan kabilar Igbo na da damar ci gaba da zama.

A cewar Ganduje “babu wanda y aba da wa’adin barin gari a Kano. Ko lokacin da suka ji labara, su (‘yan Igbo) sunce babu inda zasu sannan kuma muma mun fada masu cewa babu inda zasu.

“Don haka, al’amari ne da mu ‘yan Kano, muke son nuna misali na hadin kan kasa.

“Don haka a Kano muna magana da mutanen kuma zamcen gaskiya mun share al’amarin yan kasa da baki.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel