Kwanan Buhari 20 bai san inda yake ba, yana bukatar addu'a - Gwamna Fayose

Kwanan Buhari 20 bai san inda yake ba, yana bukatar addu'a - Gwamna Fayose

- Kawo yanzu dai Shugaba Buhari ya shafe kimanin kwanaki 53 kenan a wajen Najeriya domin neman lafiya amma har yanzu babu wanda ya san halin da yake ciki.

- Gwamnan na Ekiti a cikin wani sakon sa da ya fitar ta hannun mai bashi shawara ta musamman yace shima kamar ko wane dan Najeriya ba ya fatan mutuwa ga shugaban amma dai yana da bukatar sanin halin da yake ciki.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Gwamnan ya ci gaba da cewa sakon barka da Sallah da shugaban ya aike bai da wani tasiri don kuwa anayin kokarin a boye ainihin halin da yake cikine kawai.

Gwamnan yace: "A iya sani na dai shugaba Buhari yana da matsala wajen yadda yake magana sannan kuma hasali ma dai kusan kwanan shi 20 bai san a inda yake ba tun 6 ga watan Juni a can asibitin."

Kwanan Buhari 20 bai san inda yake ba, yana bukatar addu'a - Gwamna Fayose

Kwanan Buhari 20 bai san inda yake ba, yana bukatar addu'a - Gwamna Fayose

"Muna kuma da masaniyar cewa har uwar gidan sa taje duba shi amma ba'a bar ta ta ganshi ba saboda tsanantar ciwon nashi". Yace.

Daga karshe sai ya kalubalanci dukkan wanda yake da wani bayani akasin hakan da ya fito ya fada a cikin awa 48.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel