Biyafara: Wani babban ‘Dan PDP yayi watsa-watsa da Kanu

Biyafara: Wani babban ‘Dan PDP yayi watsa-watsa da Kanu

– Adeyanju Deji yayi kaca-kaca da jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

– Deji yace yana goyon bayan Inyamuri yayi mulki a kasar

– Sai dai ba ya tare da Nnamdi Kanu wajen wannan tafiyar ta shi

Deji babba ne a Jam’iyyar PDP kuma yace tir da dabi’ar Nnamdi Kanu. Adeyanju Deji yace Kanu zai halaka Jama’a kamar yadda Ojukwu yayi. Ko dai yace har gobe yana sa ran ganin Inyamuri yayi mulki a Najeriya.

Biyafara: Wani babban ‘Dan PDP yayi watsa-watsa da Kanu

Babban Dan PDP yayi tir da dabi’ar Nnamdi Kanu

Wani tsohon Darektan harkokin yada labarai a kafafen zamani Adeyanju Deji ya soki Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu inda yace sai an yi hattara don kuwa zai jefa Jama’a a rami kamar yadda su Ojukwu da Obasanjo su ka yi.

KU KARANTA: Kano za ta cigaba da hada kan Najeriya - Ganduje

Biyafara: Wani babban ‘Dan PDP yayi watsa-watsa da Kanu

Ba na goyon bayan Kanu Inji Ade Deji

Deji yace yana sa ran ganin Inyamuri yayi mulki kasar nan amma ba da hayaniya da zagin kowa kamar yadda Kanu ya dauka ba. Deji yace bai ganin mutuncin Kanu wanda ya kira da yaro ko na nan kusa ya kuma yi Allah-wadai da shi.

Kiristocin Katolika da ke Enugu na zaune cikin dar-dar game da wa’adin da wasu Matasan Arewa su ka ba Inyamuran da ke Yankin na su bar Arewa. Shigen haka ne dai ya kawo rikicin Biyafara a baya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Anya Najeriya za ta kara dawo daidai kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel