Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

- Rundunar sojojin Najeriya ta kama wani mai shekaru 20 wanda ake zargi ‘yan ta’adda Boko Haram a Buni Gari

- Isah Garba a lokacin da dakarun suka kama shi bai cikin hankalin sa domin wasu kwayoyin da ya sha

- Sojojin sun dakile wasu bama-bamai da kungiyar Boko Haram ta dasa a hanyan shanun Wajiro-Mallam Kuramti

Sojojin na 27 Task Force Brigade wadanda aka tura a Buni Gari sun kama wani da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram mai suna Isah Garba dan shekaru 20 yayin da sojojin ke sintiri a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni 2017 a yankin.

Bincike na farko da aka gudanar a kan Isah bai yi wani tasiri ba saboda yawan wasu kwayoyi da yasa. Amma yazu haka al’amarin ya fara canzuwa yayin da ya fara ba jami’an tsaro hadin kai.

KU KARANTA: Yadda Yansanda suka yi sanadiyyar mutuwar dalibin kwalejin kimiyya dake Kaduna

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

Daya daga cikin sojojin 27 Task Force Brigade

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a wata bangare kuma Sojojin na 29 Task Force Brigade yayin da suke sintiri a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni 2017, dakarun sun gano wasu bama-bamai da kungiyar Boko Haram ta dasa a hanyan shanun Wajiro-Mallam Kuramti, wanda tuni tawagar sojojin ta cire da kuma tayar da wasu.

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

An gano wasu bama-bamai da kungiyar Boko Haram ta dasa

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

Sojoji na 27 Task Force Brigade a lokacin da suke sintiri a Buni Gari

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

bama-bamai da kungiyar Boko Haram ta dasa

Boko Haram: Rundunar sojan Najeriya ta cafke wani Boko Haram a Buni Gari (Hotuna)

Kayan hada bama bamai na kungiyar Boko Haram

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel