Auren wuri na kawo koma bayan tattalin arziki

Auren wuri na kawo koma bayan tattalin arziki

- Bankin duniya ta ce aurar da 'ya'ya mata da wuri na kawo koma bayan tattalin arziki

- A cewar rahoton dakatar da auren wuri ga yara mata zai taimaka kwarai gurin dawo da martabar tattalin arziki

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar ya ce aurar da mata da wuri na kawo koma bayan tattalin arzikin duniya.

Rahoton ya ce auren wurin yana janyo asarar biliyoyin dala.

A cewar rahoton idan aka daina yi wa 'yan mata auren wuri, za a samu karin walwala da habakar tattalin arziki.

Rahoton ya bayar da misali da kasar Uganda wadda aka samu raguwar haife-haife lamarin da ya sa kasar ke iya tanadin $2.4bn.

KU KARANTA KUMA: An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

Auren wuri na kawo koma bayan tattalin arziki

Auren wuri na kawo koma bayan tattalin arziki

Dr Adamu Isa, wani masani kan harkokin da suka shafi rayuwar mata, kuma shugaban sashen kula da lafiyar al'umma a jami'ar tarayya da ke Dutse a Najeriya, ya shaida cewa wadanda suka fitar da rahoton suna kallon rayuwa ta fuskoki da yawa.

Yace: "Daya daga cikin su shi ne da a ce ba a yiwa yarinya aure da wuri ba, an bar ta ta yi karatun jami'a za a dama da ita, ta samu aikin yi.

"Sannan kuma za ta iya rike babban mukami da za ta iya tallafawa iyali da danginta".

Sai dai wasu 'yan kasar na ganin auren wuri yana da amfani domin kuwa wasu mazan za su bar ta ta yi karatu har ma ta samu akin da za ta taimake shi da ma iyalinta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel