An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

- An yi bikin wata mata, Alimiha Seiti da ta fi tsufa a duniya a kasar China

- An haifi wannan matar ne a watan Yuni 15, 1886 a yankin Kashgar da ke yammacin Xinjiang Ugiranci ta China

- Likita Abdul Rusuli ya ce tsohuwar na cikin isashen lafiyar

Alimiha Seiti wanda ta ce an haife ta a shekara 1886 wanda ya sanya ta mafi tsufa a duniya. Wannan matan wanda aka yi bikin ranar haihuwar ta na cika shekaru 131 a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni tare da jikokinta 56.

A cewar rahoton jaridar Mirror ta China, ta bayyana cewa an haifi Alimiha Seiti a watan Yuni 15, 1886.

KU KARANTA: Ya kashe Uwargijiyarsa sakamakon kin amincewa da soyayyarsa

Alimiha wanda ta ke zaune a Shule County a yankin Kashgar da ke yammacin Xinjiang Ugiranci ta China, ta ce ta na son magana da mutane kuma ta na shawar yin wata.

An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

Alimiha Seiti mai shekaru 131

NAIJ.com ta ruwaito cewa, likitan da ke lura da ita, Abdul Rusuli wanda ya dubi lafiyarta a ranar bikin haihuwar ya ce tsohuwar na cikin isashen lafiyar.

An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

Matar da ta fi tsufa a duniya da wata 'yar uwanta

An yi bikin ranar haihuwar wanda ta fi tsufa a duniya mai shekaru 131 da jikoki 56 (Hotuna)

Alimiha Seiti da wata jikan ta

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel