LABARI DA DUMI DUMI: Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane ya kai karan Sufeto-janar na 'yan sanda Kotu

LABARI DA DUMI DUMI: Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane ya kai karan Sufeto-janar na 'yan sanda Kotu

- Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane wato Evan ya kai karan Babban Sufeto na 'yan sanda da wasu jami’an tsaro Kotu

- Evan na zargin jami’an tsaro da ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi kotu ba

- Evan ya ce idan ba za a gurfanar da shi kotu ba zai a tsake shi

Babban biloniyan nan da ake zargi da garkuwa da mutane Chukwudumeme Onwuamadike wato Evans, ya kai karan babban Babban Sufeto na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris da kuma wasu mutane uku a babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan tsare shi da ake yi a bisa zargin da ba bisa ka'ida.

A cikin wadanda madugun da ake zargi da garkuwa da mutane zai kai kara sun hada da 'yan sandan Najeriya, kwamishinan' yan sandan jihar Legas, tawagar masu dakile ‘yan fashi da makami wato Special Anti-Robbery Squad da kuma rundunar 'yan sandan jihar Legas.

KU KARANTA: YANZU YANZU: Suntai tsohon gwamnan Taraba da ya yi hatsarin jrgin sama ya mutu a Amurka

LABARI DA DUMI DUMI: Madugun da ake zargi da garkuwa da mutane ya kai karan Sufeto-janar na 'yan sanda Kotu

Babban biloniyan da ake zargi da garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, madugun da ake zargi da garkuwa da mutane na neman kotu ta umurni jami’an tsaro cewa a gurfanar da shi gaban kotu idan aka same shi da wata laifi ko kuma su sake shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel