‘Yan kabilar Igbo mazauna jihar Kano sun zama asali ‘yan kasa yanzu – Inji gwamna Ganduje

‘Yan kabilar Igbo mazauna jihar Kano sun zama asali ‘yan kasa yanzu – Inji gwamna Ganduje

- Gwamnan Jihar Kano ya ceduk ‘yan kabilar Igbo mazaunan jihar Kano sun zama asali ‘yan kasa

- Ganduje ya bayyana cewa shine yasa ‘yan majilisar jihar dakatar da bincike kan Sarkin Kano

- A cewar Gwamnan, jihar Kano zata ci gaba a sahun gaba wajen hada kai ‘yan Najeriya

Bayan umarnin ficewa daga jihohin arewa da kungiyoyin matasan arewa suka wa ‘yan kabilar Igbo kwana kwanan nan, gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ‘yan kabilar Igbo da ke jihar Kano da kuma kowa da kowa a yanzu haka sun zama ‘yan asalin Kano.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Ganduje yayi wannan bayani ne a lokacin da ya ziyarci sakatariya na jama'iyyar APC mai mulki a birnin Abuja a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni.

Ganduje ya kuma yi magana kan rashin jituwa da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi , ya ce: “Ban san da zargin da ake wa ‘yan majalisar jihar ba, amma na san cewa ni da kaina na rubuta musu wasika inda na nema su dakatar da gudanar da bincike kan Sarkin Kano saboda wasu mayan kasar sun sa baki ga al’amarin.”

‘Yan kabilar Igbo mazauna jihar Kano sun zama asali ‘yan kasa yanzu – Inji gwamna Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

KU KARANTA: Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa

" Na ambata dalilai da yasa na bukaci ‘yan majalisar jihar dakatar da binciken a cikin wasika na kuma an wallafa ta a kafofin yada labarai na kasa”.

Gwamnan ya cigaba da cewa jihar Kano zata ci gaba a sahun gaba wajen hada kai ‘yan Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel