Karuwai da Mabarata 789 aka fatattaka daga babban birnin tarayya – Minista

Karuwai da Mabarata 789 aka fatattaka daga babban birnin tarayya – Minista

- Ministan babban birnin tarayya Abujaya ce sun kori karuwai da mabarata sama da 789 daga babban birnin tarayya

- Ya sun yi hakan ne a shekarun biyun da Buhari ya yi a kan mulki

- Bello ya ce yawancin su an mayar da su ne jahohin su bayan an yi yunkurin shiryar da su

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello ya ce sun kori karuwai da mabarata sama da 789 daga babban birnin tarayya Abuja a ciki shekaru biyun da shugaba Buhari ya yi mulki.

A wata hira da ya yi da manema labarai, Bello ya ce yawancin su an mayar da su ne jahohin su bayan an yi yunkurin shiryar da su.

Sakatariyar hukumar SDS Irene Adebola Elegbede wacce ta wakilci ministan ta ce duk da haka su na fuskantar kalubalai wajen kakkabe sana’ar daga babban birnin tarayyan.

Ta ce a duk lokacin da suka kore su daga wannan yanki, sai su bullo a wani ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma ta koka akan yadda maza ke sanya baki da rokon su su saki karuwai a duk lokacin da aka kama su, inda ta ce ba za su samu nasara ba idan wadannan maza ba su basu hadin kai ba.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Suntai tsohon gwamnan Taraba da ya yi hatsarin jrgin sama ya mutu a Amurka

Karuwai da Mabarata 789 aka fatattaka daga babban birnin tarayya – Minista

Karuwai da Mabarata 789 aka fatattaka daga babban birnin tarayya – Minista

Ta ci gaba da cewa a duk lokacin da suka kama su, su kan koya masu sana’o’i sannan a basu jari kafin a sake su, amma da zaran an sake su sai su koma kan titina.

A karshe ta yi kira ga majalisa da ta gaggauta kafa dokokin da za su taimaka masu wajen dakile ayyukan mabarata, bata gari da karuwai da suka cika titinan babban birnin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel