YANZU YANZU: Suntai tsohon gwamnan Taraba da ya yi hatsarin jrgin sama ya mutu a Amurka

YANZU YANZU: Suntai tsohon gwamnan Taraba da ya yi hatsarin jrgin sama ya mutu a Amurka

- Mista Danbaba Suntai, tsohon gwamnan jihar Taraba, ya mutu

- Ya samu mummunan rauni a lokacin da jirgin say a fadi a ranar 25 ga watan Oktoba, 2012 a Yola, babban birnin jihar Adamawa

- An rahoto cewa ya shiga wani yanayi tun bayan afkuwar hatsarin na jirgin sama

Mista Danbaba Suntai, tsohon gwamnan jihar Taraba, ya mutu.

Gwamna Danbaba Suntai ya samu mummunan rauni a lokacin da jirgin sa ya fadi a ranar 25 ga watan Oktoba, 2012 a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Ya samu tabuwar hankali tun bayan hatsarin kuma a yanzu an tabbatar da mutuwar sa a kasar Amurka.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Suntai ya shiga wani yanayi tun bayan afkuwar hatsarin na jirgin sama a ranar 25 ga watan Oktoba, 2012 a jihar Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

Mista Emmanuel Bello wani tsohon kwamishinan labarai a jihar, ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan a Abuja a ranar Laraba.

Bello, wanda ya yi aiki lokacin Suntai, ya ce, “tsohon gwamna ya mutu a kasar Amurka.”

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel