Shugabannin Yarbawa na shirya kaidin gadarwa Osinbajo kujeran shugaban kasa, Muhammadu Buhari – Matasan Arewa sunyi gargadi

Shugabannin Yarbawa na shirya kaidin gadarwa Osinbajo kujeran shugaban kasa, Muhammadu Buhari – Matasan Arewa sunyi gargadi

Wata gamayyar kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya tayi zargin cewa shugabannin kabilar Yoruba na shirya wata sabuwar kaidin gadarwa Farfesa Yemi Osinbajo kujeran shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma hakan ba zaiyi yiwu ba.

Kungiyar tayi wannan gargadi ne a wata jawabin da Muhammad Shehu da Tanko Abdullahi suka rattaba hannu inda suka ce ko ta kaka sai Arewa ta share wa’adin shekaru 8 a karagar mulki.

Yayinda suke zargin shugabannin Yoruba na kokarin hana shugabanci dawowa Arewa, matasan sun lashi takobin cewa ba zai taba yiwuwa ba komin kaidi sa siyasar da zasu shirya.

Wani sashen jawabin yace: “ Muna sane da cewa dukkan soke-soken dda ake yiwa Buhari a kafafen yada labarai da Yarbawa keyi kuma mutanen kudu suke yadawa domin bata sunan Arewa saboda yaronsu, Yemi Osinbajo, ya zama shugaban kasa ne. Amma zasuji unya idan Allah ya yarda.”

Shugabannin Yarbawa na shirya kaidin gadarwa Osinbajo kujeran shugaban kasa, Muhammadu Buhari – Matasan Arewa sunyi gargadi

Shugabannin Yarbawa na shirya kaidin gadarwa Osinbajo kujeran shugaban kasa, Muhammadu Buhari – Matasan Arewa sunyi gargadi

“Zamu tsaya tsayin daka domin tabbatar da cewa Arewacin Najeriya ta cika wa’adinta na shekaru 8 ko kuma ta cigaba, idan masu kiraye-kirayen fita daga kasa basu fi taba.”

KU KARANTA: YAn bindiga sun budewa babban jami'in EFCC wuta

Ya siffanta kabilar Yoruba a matsayin kabila maras godiya, bayan an basu mulki kyauta a shekaran 1999 saboda saka masu da abinda ya faru da Abiola a shekarar 1993. Abin kunya ne kuma da ban takaici cewa suna kokarin yaudaran Arewa ta hanyar goyon bayan masu kirayen fita daga Najeriya.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel