Wata mata ta haifi kifin tarwada a coci bayan watanni 16 da daukar ciki

Wata mata ta haifi kifin tarwada a coci bayan watanni 16 da daukar ciki

Abun al’ajabi baya karewa kamar yadda aka rahoto cewa wata mata ta haifi kifin ruwa wato tarwada a wani coci dake Afrika ta Kudu.

Mutanen Afrika ta Kudu sun shiga alhini yayinda wata mata mai cikin watanni 16 ta haifi kifin ruwa bayan ta halarci wani taro da fasto din Najeriya, Samuel Akinbodunse ya shirya.

NAIJ.com ta tattaro cewa matar wacce bata ga alamun nakuda ba bayan watanni 16 da daukar ciki ta tunkari bawan Allah da yay i wasu zantuka a rayuwarta sannan kuma a take ta fara nakuda.

KU KARANTA KUMA: Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

Wata mata ta haifi kifin tarwada a coci bayan watanni 16 da daukar ciki

Wata mata ta haifi kifin tarwada a coci bayan watanni 16 da daukar ciki

An rahoto cewa an dauki atar wacce ba’a fadi sunan ta zuwa asibiti cikin gaggawa amma abun mamaki, sai ta haifi tarwada a maimakon mutun.

An kuma rahoto cewa matar ta dade tana rokon Allah ya bata haihuwa har ta kai ziyara wani coci sannan kuma aka nemi ta biya naira miliyan daya wanda bayan nan ne ta samu ciki.

Kalli bidiyon faston a kasa:

Bayan ta samu ciki, ta bayyana cewa an fada mata ta zo da misalin karfe 12 na dare domin a fada mata lokacin da zata haihu.

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com a kasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel