An harbi wani babban jami'in EFCC a Ribas

An harbi wani babban jami'in EFCC a Ribas

- An budewa wani babban mai binciken hukumar EFCC, Austin Okwor wuta

- An harbawa Okwor harsasai da dama a garin Fatakwal, jihar Ribas

- Wanni hari ya faru ne bayan Okwor ya samu sakonnin barazana tattare da ayyukanshi

An kaiwa wani babban jami’in hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Austin Okwor, harin kisa a ranan Asabar, 24 ga watan Yuni a Fatakwal, jihar RIbas.

Wata jawabin da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya saki yace Austin Okwor ya tsallake rijiya da baya yayinda wasu yan bindiga suka bude masa wuta a jihar ta RIbas.

YANZU-YANZU: Yan bindiga sun budewa wani babban jami'in EFCC wuta

YANZU-YANZU: Yan bindiga sun budewa wani babban jami'in EFCC wuta

Wilson Uwujaren yace yayindaAsutin ya tashi aiki ranan Asabar, kawai sai suka bude masa wuta, daga baya aka kaishi wata asibiti a garin Fatakwal sanadiyar harsasai da suka shiga jikinsa.

Yace:” Okwor daya daga cikin ma’ikatanmu masu binciken wasu manyan barayi ne wanda ya kunshi alkalai.”

KU KARANTA: Shugaban asibitin ciwon kunne ya rasu a Masallaci

" Kafin a kai masa wannan hari, ya kasance yana samun sakonnin barazana musamman a wata Mayu wanda ya kai kara ofishin yan sanda.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel