Dalilan da yasa mafi yawancin yan arewa ke fushi da Kabilar Ibo - Doyin Okupe.

Dalilan da yasa mafi yawancin yan arewa ke fushi da Kabilar Ibo - Doyin Okupe.

- Kabilar Ibo suna ma mutanen arewa kallon cin ma zaune wanda ke bata ma yan arewan rai - inji Doyin Okupe

- Wasu yan arewa har yanzu suna jin haushin kashe Sir Ahmadu Bello da Nzegwu Kaduna dan kabilar ibo yayi

Mai taimaka ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan hulda da jama'a Doyin Okupe ya zayyana wasu dalilai da yasa mafi yawancin mutane arewa ku fushi da kabilar ibo.

Doyin din dai yace ya gano wadandan dalilian ne bayan bincike da yayi a arewaci da kudu masa gabashin Najeriya.

Ya cigaba da cewa, ra'ayoyin yan arewan ya kasu gida biyu ne akan kabilar ibo, akwai wanda suke ganin zaman kabilar ibo a arewa nada hadari sannan akwai wanda suke ganin zaman kabilar ibon a arewar ba wata matsala bace.

Dalilin da yasa mafi yawancin yan arewa ke fushi da Kabilar ibo - Doyin Okupe.

Dalilin da yasa mafi yawancin yan arewa ke fushi da Kabilar ibo - Doyin Okupe.

Ya kara da cewa "mafi yawancin yan arewan suna kyamatan kabilar ibon ne domin a ganin su kabilar ibon zasu rika taso da maganar ballewa daga Najeriya a duk lokacin da suke ganin ana yi musu warriya a kasar. "

A cikin wani sako kuma da aike da shafin sa na facebook. Yace "Yan arewa da yawa suna fushi da kabilar ibo akan kashe tsohon shugaba na arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan sokoto da dan kabilar ibo Nzegwu Kaduna yayi a lokacin juyin mulki.

"Dumbin yan arewa kuma suna jin haushin yadda kabilar ibo ke fadin cewa yankin arewa ce matsalar da ke damun Najeriya kuma arewacin kasar bata tsinana komai wajen habbaka tattalin arziki kawai sun zama ci ma zaune.

"Wannan tunanin yana da karfi kuma ya mamaye manya da yara na arewa."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel