Yadda Gwamna Abdulaziz Yari ya sayi makeken gidan $1m a Amurka

Yadda Gwamna Abdulaziz Yari ya sayi makeken gidan $1m a Amurka

- Gwamna Abdulaziz ya sayi kayataccen gida a kasar Amurka bayan hawan shi gwamnati da shekara biyu

- Ya sayi gidan akan $950,000 lakadan ba ajalan ba.

- Gwamna Yari ya mallaki asusun banki a kasar waje.

Sahara Reporters sun bayyana bayan shekara biyu da hawan Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari mulki an same shi da ya saya gida a Amurka a kan zunzurutun kudi kimanin dala miliyan daya.

Takaddun gidan da aka samu daga Circuit Court of Prince George’s County, Maryland, USA ne suka nuna Gwamna Yari shine mallakin gidan wanda ya saya a hannun Kamapanin K Hovanian Hamptons bayan sun canja sunan su daga Real Property Holding a shekarun baya da suka gabata.

Yadda Gwamna Abdulaziz Yari ya sayi makeken gidan $1m a Amurka.

Yadda Gwamna Abdulaziz Yari ya sayi makeken gidan $1m a Amurka.

Gwamna Abdulaziz Yari ya biya tsabar kudi dala dubu dari da hamsin. kuma takaddun sun nuna Gwamnan ya biya wa gidan haraji na wasu kudade. Kuma har ila yau yana kan biya wa gidan haraji, wanda suka bada alamar Gwamnan yana da mallakin asusu a kasar ketare duk da ya saba hukumar Code Of Conduct.

Dokar hukumar Code of Conduct ta haramtawa wasu manyan shuwagabanni da suka hada da Shugaban Kasa, mataimakin shugaban Kasa, Gwamna, mataimakin gwamna da Kwamishinoni mallakar asusu a kasashen ketare.

A watannin da suka gabata an samu labarin Gwamnan yana gina Otal a Jahar Legas. Yayin da Gwamnan ya musanta hakan cewa ma shi bai mallaki Otal ba bare fili.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel