An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

Kungiyar gudun hijran duniya wato International Organisation for Migration, IOM, ta alanta ceton akalla mutane 600 tun watan Afrilu 2017 a Sahara.

Kungiyar majalisar dinkin duniya ta kuma sanar da cewa mutane 52 yawancin yan Najeriya, Gambiya, Senegal da Cote d’Ivoire, sun hallaka a wurin, game da cewar jawabin da ta saki ranan Talata.

“Muna fadada kokarinmu wajen taimakawa yan gudun hijra a arewacin Agadez, hanyar iyakan Nijar da Libya.

“Tun daga farkon wannan shekara, munata samun kiraye-kiraye na ceton rayukan wadanda suka dau hanyar, “ Ma’aikaci Giuseppe Loprete,ya bayyana hakan.

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

An tsinto gawawwakin yan gudun hijra 52 a Sahara yayinda aka ceto 600

Game da cewarsa, wata yar shekara 22 ce kawi ta tsira a cikin wadanda aka je ceto a ranan 28 ga watan Mayu. Ta bar Najeriya ne a watan Afrilu domin ketarawa Turai.

KU KARANTA: Kannywood: Safiya Mus tayiwa sauran yan matan fim wa'azi

“Akwai yan gudun hijra 50 akan mota yayinda suka nufi Libya daga Agadez, amma mutane 6 kawai sukr raye cikinsu,” Loprete yace.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel