An bankado yan Najeriya 29 gida sanye da mari daga Turai

An bankado yan Najeriya 29 gida sanye da mari daga Turai

Kasar Sweden, Norway da Spain, da ke nahiyar Turai sun bankado ya Najeriya 29 da yan kasar Togo 2 daga kasashensu.

Wadanda aka turo sun kunshi maza 27 da mata 2. Sun sauka Najeriya da safiyar Talata, 27 ga watan Yuni sanye da mari.

Jirgin da akayi musu shata mai lamba EC-IZO ta sauka a babban filin jirgin Murtala Muhammad da ke Legas misalin karfe 6.45 na safe.

Wani ma’aikacin filin jirgin saman yace an dauresu da mari saboda zasu iya zama matsala ga jami’an hukumar shiga da fice da a cikin jirgi.

Kasashen Turai 3 sun bankado yan Najeriya 29 gida sanye da mari

Kasashen Turai 3 sun bankado yan Najeriya 29 gida sanye da mari

Ina mai tabbatar muku da cewa mazajen da aka sanyawa mari, an dauresu ne saboda ana tsoron abinda zasu iya yi domin nuna bacin ransu , amma an cire marin bayan sun fara tafiya,.”

“Da badin haka ba, basuyi niyyar dawowa Najeriya ba, ransu a bace yake saboda cin zarafinsu d akayi a hannun ma’aikatan.”

“Daya daga cikin jami’an hukumar shiga da fice da kuma yan sanda ya fada mini cewa an ci zarafinsu sosai."

KU KARANTA: Dino Melaye ya kai kara kotu

Kana wasu daga cikinsu na daure tun shekaran da ya wuce kuma an hanasu saduwa da iyalai da abokai har sai lokacin dawo da su Najeriya yayi.

Kakakin hukumar yan sandan filin jirgin masan, DSP Joseph Alabi, yace jami’an hukumar shiga da fice, hukumar hana safarar mutane da hukumar yan sanda ne suka tarbesu.

Alabi yace 9 daga cikin wadanda aka bankadona da laifukan ta’amuni da muggan kwayoyi kuma an mikasu ga hukumar NDLEA, yayi wasu biyu kuma an mikasu ga hukumar yan sanda.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel