Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

- Dangote ya yi tsokaci a kan wa'adin da wasu matasan Arewa suka ba 'yan Igb o mazauna yankin

- Ya bayyana hakan a matsayin rashin aikin yi

- Ya sha alwashin samar da ayyukan yi ga matasa da zaran ya kammala aikin matatar man fetur din sa

Mai kudin Afrika kuma Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana nasa ra’ayin a kan wa’adin da wasu kungiyoyin matasan Arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo mazauna yankin.

A yayin da ya karbi bakuncin ‘yan makarantar koyar kasuwanci ta Jihar Lagas LBS a matatar man fetur din shi dake yankin Ibeju-Lekki da ke jahar, Dangote ya bayyana al’amarin a matsayin rashin aikin yi.

KU KARANTA KUMA: Cikar Buhari kwanaki 50 a Landon: ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu

Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Jaridar The Nation ta rahoto shi ya na cewa “Na yi mamaki da kowa ya fara magana akan wannan shirmen. Me ya sa muke tattaunawa akai?

“Tabbas dole ne a samu irin wanann a duk inda ake fama da rashin ayyukan yi. Wadanda ba su da abun yi su kan nuna bacin rai daban-daban.

“Mun fahimci abubuwan da ke sa ransu ke baci, amma wannan ba dalili bane tunda sun ki neman abun yi.”

Dangote ya tabbatar da cewa idan aka kammala aikin matatar man fetur din na shi, zai samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel