Karin kudin makaranta: Majalisar dattijai zata aikawa jami'oi 38 da takardar sammaci

Karin kudin makaranta: Majalisar dattijai zata aikawa jami'oi 38 da takardar sammaci

- Majalisar dattijai ta ce zata kirawo jami'oin da suka kara kudin makaranta

- Jamii'oi 38 ne dai suka yi karin a cikin shekaru 2 da suka wuce

- Majalisar ta ce zata neme su ne idan ta dawo daga hutun Sallah

Majalisar dattijai a Najeriya tace zata aike wa mataimakan shugabannin jami'oin Najeriya 38 da takardar sammaci saboda karin kudin makarantar da sukayi wa daliban su.

Shugaban kwamitin majalisar dattijan mai kula da harkokin makarantun gaba da sakantare da kuma hukumar nan ta TETFUND Sanata Barau Jibrin (APC Kano) ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.

Karin kudin makaranta: Majalisar dattijai zata aikawa jami'oi 38 da takardar sammaci

Karin kudin makaranta: Majalisar dattijai zata aikawa jami'oi 38 da takardar sammaci

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sanata Jibrin ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake tsokaci game da wani labarin da kungiyar malaman jami'oin ta ta kasa watau ASUU ta fitar inda take fallasa yadda jami'oi 38 mallakin gwamnatin tarayya suka kara kudin makarantar su a cikin shekaru biyu da suka shude.

Kungiyar ta ASUU har ila yau ta danganta karin kudin ga rashin fifiko da fannin ilimin ya samu a karkashin wannan gwamnatin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel