Yadda Yansanda suka yi sanadiyyar mutuwar dalibin kwalejin kimiyya dake Kaduna

Yadda Yansanda suka yi sanadiyyar mutuwar dalibin kwalejin kimiyya dake Kaduna

Wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha dake Kaduna ya rigamu gidan gaskiya jim sakamakon haduwa da yayi da Yansanda a ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni.

Dalibin mai suna Benjamin Wankaa inkiya Mc Cedar ya kasance kuma yana harkar kula da sha’anin bukukuwa a matsayin sana’arsa, sa’annan dan aji 3 uku ne a kwalejin na Kaduna, tsangayar ma’adanan kasa.

KU KARANTA: Kalli yadda Saniya tayi sama sama da wani mutumi a Sakkwato

Wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da Mc Cedar tare da yan uwansa ke hanyarsu ta dawowa da daddare daga wani bushasha da aka shirya, inda Yansanda suka tare su akan hanyuar ta zuwa gida.

Yadda Yansanda suka yi sanadiyyar mutuwar dalibin kwalejin kimiyya dake Kaduna

Mc Cedar

NAIJ.com ta gano bayan su Mc Cedar da yan uwan nasa sun gabatar da kansu ga Yansandan a matsayin daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, sai suka nuna musu shaidar dalibta.

Amma duk da haka sai Yansandan suka yi awon gaba da mutane hudu daga cikinsu, amma basu tafi da Mc Cedar ba, a nan ne fa sauran Yansandan da aka bari suna tsare da su Mc Cedar suka ce wai yana kokarin tserewa.

Yadda Yansanda suka yi sanadiyyar mutuwar dalibin kwalejin kimiyya dake Kaduna

Kwalejin kimiyya da fasaha

Abinka da jami’in tsaro, sai dai kawai da safe aka kwashi gawar Mc Cedar a gefen hanya ranga ranga sun kakkarya masa hannuwa da kafafu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin dansanda abokin kane?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel