Cikar Buhari kwanaki 50 a Landon: ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu

Cikar Buhari kwanaki 50 a Landon: ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu

- A ranar Litinin, 26 ga watan Yuni ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika kwanaki 50 da tafiya birnin Landan

- Shugaban kasar ya bar gida Najeriya zuwa birnin Landan domin ci gaba da jinya

- Har yanzu babu tsayayyen magana a kan ranar dawowar shi kasar

A ranar Litinin, 26 ga watan Yuni ne shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika kwanaki 50 da tafiya birnin Landan don ci gaba da jinya.

‘Yan Najeriya sun yi amfani da wannan dama wajen yin sharhi game da ci gaba da kasancewar shugaban kasar a Landon ba tare da sanin ranar dawowar sa ba.

A baya tafiyar da Buhari ya yi a ranar 19 ga watan Janairu, ya dawo ne a ranar 10 ga watan Mayu, shugaban ya kwashi kwanaki 50 ne cif, duk da cewa kwanaki 10 ya dauka na hutu.

A wancan tafiyar, kamar yadda aka yi a wannan, shugaban ya mika ragamar mulki ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo kamar yadda kundin tsarin Mulkin kasa ya tanadar.

KU KARANTA KUMA: Kiranye: Dino Melaye ya garzaya kotuKiranye: Dino Melaye ya garzaya kotu

Cikar Buhari kwanaki 50 a Landon: ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu

Cikar Buhari kwanaki 50 a Landon, ‘Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu

Sai dai kuma a kowacce tafiya, makusanta shugaban kasar da wadanda ke da alhakin bayyana wa ‘yan Najeriya halin da yake ciki sun gaza yin haka, kai hasali ma lamarin ya fi sauki a wancan tafiyar, inda ‘yan Najeriya ka iya tsintar batutuwa anan da can su yi inkari akan halin da shugaban ke ciki.

A cikin kwanaki 177 da aka shafe a wannan shekara, shugaba Buhari ya kwashi kwanaki 101 kenan yana samun kulawar likitocin sa a birnin Landon.

Duk da sakon muryar da shugaban ya fitar a ranar Sallah karama da aka gabatar a ranar 24 ga watan Yuni, wannan bai kwantar da hankulan jama’a ba. A ra’ayin wasu ma sakon muryar ya kara tayarwa ‘yan Najeriya hankali game da lafiyar shugaban kasar su.

A hirar da Jaridar Premium Times ta yi da wasu ‘yan Najeriya a ranar Litinin 26 ga watan Yuni, sun bayyana ra’ayoyi daban-daban game da wannan hali da kasar ta riski kanta a ciki.

Wani mai nazari akan harkokin tsaron kasar, Muktar Dan’iyah ya bukaci ‘yan Najeriya da su matsawa Gwamnati har sai ta yi karin bayani akan halin da shugaban kasar ke ciki.

Ya ce kasancewar iyalin shugaban sun yi bikin Sallah a Najeriya ba tare da shugaban ba, wani abu ne da ya kamata ‘yan Najeriya su yi duba akai.

Wani lauya mazaunin jahar Lagos, Liborous Oshoma kuwa tambayoyi biyar ya bukaci kowanne dan Najeriya ya tambayi wannan gwamnati:

Menene matsayin lafiyar shugaban kasa? Wa yake biyan kudaden maganin shi? Idan daga kudaden ‘yan Najeriya ake biyan maganin, nawa aka kashe izuwa yanzu?

Idan shugaban ya dawo gida Najeriya, a halin da yake ciki, shin zai iya ci gaba da mulkin kasar, ko kuwa zai dawo ne ya koma bayan wani dan lokaci?

Me yasa ba a duba yiwuwar yin murabus na shugaban?

Sai dai kuma duk da wannan maganganu, wasu ‘yan majalisun tarayya sun nuna cikakken goyon bayan su ga shugaba Buhari.

Razak Atunwa, wani dan majalisar wakilai daga jihar Kwara ya ce a ra’ayinsa gwamnati ta na tafiya sumul yadda ya kamata saboda yadda shugaba Buhari ya bi ka’idar tsarin mulkin kasa.

A nashi bangaren kuwa, Sunday Karimi wani dan majalisa daga jahar Kogi dan jam’iyyar PDP haka ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su gode Allah da yunkurin da shugaban ya yi kafin ya bar Najeriya.

A cewar shi “shugaban bai yi fatan haka ta faru da shi ba.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel