Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa

- Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa albarkacin bikin sallah karama,

- Yace tuni Gwamnatinsa ta kafa kwamiti da zai fitar da sunayen wadanda alfarmar zata shafa, kwamitin zai kammala aikinsa a cikin makonni Biyu.

Fursunoni 200 za'a fito dasu ne daga gidan fursuna na tsakiyar jihar a yayin da ragowar 300 kuma za'a fito dasu ne daga gidan fursuna na Goron Dutse da sauransu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a sanarwar da daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnatin jhar, Salihu Tanko Yakasai ya fitar, yace Gwamnan yayi rangadin ne tare da rakiyar ministan cikin gida Laftanar Janaral A.B. Dambazau (mai murabus).

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yiwa fursunoni 500 afuwa

Gwamna Ganduje yace akwai kuma kwamiti na musamman da zasu bibiyi wadanda aka yankewa hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai domin yin nazarin hukuncin nasu. Kwamitin zai bawa Gwamnati shawarar abunda ya kamata ayi masu na afuwa ko akasin haka.

Dakta Ganduje ya kuma yi amfani da damar wajen ayyana sakin fursunoni 50 da Gwamnati tayiwa afuwa a lokacin bikin jihar Kano shekara 50 da kafuwa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel