Gwamnan Katsina Aminu Masari ya fitar da fursunoni 61 albarkacin sallah

Gwamnan Katsina Aminu Masari ya fitar da fursunoni 61 albarkacin sallah

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya biya kudi Naira miliyan uku da dubu dari shida da sittin da shidda (N3,666,000.00) wanda shine jimillar tarar da ake bin wasu masu kananan laifuka 61 dake gidajen yari daban daban a fadin jihar, tare da basu Naira dubu biyar kowannen su domin yin kudin motar zuwa gida.

A takardar da aka rabawa manema labarai dake dauke da sa hannun mai taimakawa Gwamna kan harkokin watsa labarai Abdu Labaran Malunfashi, an bayyana cewa Gwamna Masari ya gargade su da su guji sa kawunan su cikin al'amuran da ka iya mayar da su cikin halin da suka fita a ciki.

Gwamnan Katsina Aminu Masari ya fitar da fursunoni 61 albarkacin sallah

Gwamnan Katsina Aminu Masari ya fitar da fursunoni 61 albarkacin sallah

NAIJ.com ta samu labarin cewa biyan wannan tara yana cikin aniyar gwamnatin jihar Katsina ta ganin an kyautata wa al'umma musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah da kuma ganin an rage cunkoson dake a gidajen yari.

Tuni dai wadannan bayin Allah suka koma cikin iyalan su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel