Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

- Kungiyar IPOB ta ce ba dan siyasar da ke bata ko sisi domin gudanar da ita

- Kungiyar wadda Nnamdi Kanu ke jagoranta ta yi watsi da zargin hukumar EFCC

- Kungiyar tace mambobin ta ne ke tara mata kudin shiga ba kowa ba

Kungiyar nan ta masu tayar da kayar baya ta inyamurai masu fafutukar kafa kasar Biafra da Nnamdi Kanu ke jagoranta watau IPOB ta yi fatali da zargin da hukumar EFCC tayi mata na cewa yan siyasa ne ke bata kudin gudanarwar ta.

Kungiyar dai ta bayyana cewa zargin na hukumar EFCC baya da tushe balla makama don kuwa ita babu wani dan siyasar da ke bata ko da sisin kwabo ne a cikin harkokin gudanarwar ta.

Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

Yadda muke samun kudaden gudanarwar kungiyar mu – IPOB

NAIJ.com ta samu labarin cewa kungiyar ta IPOB tayi wannan jawabin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai inda tace yayan kungiyar ne daga dukkan fadin duniya suka tattara kudin gudanarwar kungiyar amma ba yan siyasa ba.

Kungiyar tace ita ta ma fi kyamar yan siyasar yankin na inyamurai akan kowa don haka babu yadda za'ayi su nemi wani abu daga gare su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel