Da alama jami’an tsaro ba zasu iya maganin masu aikata miyagun laifuka a jihar Neja ba - Gwamna

Da alama jami’an tsaro ba zasu iya maganin masu aikata miyagun laifuka a jihar Neja ba - Gwamna

- Gwamnan jihar Neja ya koka kan karuwar miyagun ayyuka a jihar sa

- Gwamna Bello yace jami'an tsaron dake jihar sun gaza

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello yace jihar Neja na kashe miliyoyin kudi da suka kai naira miliyan 100 a duk wata, amma basa ganin sakamakon daya dace.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan yana bayyana haka ne yayin daya karbi bakoncin Sarakunan gargajiya jihar a ranar Talata 27 ga watan Yuni, inda ya bayyana musu shifa ya fara gajiya da gazawar jami’an tsaro wajen magance matsalar yan fashi, garkuwa da mutane, kashe kashe da satar shanu.

KU KARANTA: Ina goyon bayan gwamnatin gwamna Ganduje ɗari bisa ɗari – Sarkin Kano

“Don haka nake ganin, zamu koma amfani da tsarin mu na dauri, inda sarakunan gargajiya zasu taimaka waken inganta tsaro a jihar. Ina ganin zamu karfafa sarakunan mu don cimma wannan buri namu.” Iji gwamna Bello

Da alama jami’an tsaro ba zasu iya maganin masu aikata miyagun laifuka a jihar Neja ba - Gwamna

Gwamna Bello tare da Sarkin Minna

Daga karshe, majiyar NAIJ.com ta ruwaito gwamnan yana shawartar yan Najeriya dasu dage wajen yin addu’a sakamakon duk kokarin da gwamnati keyi na kawo tsaro ya ci tura.

Da alama jami’an tsaro ba zasu iya maganin masu aikata miyagun laifuka a jihar Neja ba - Gwamna

Sarakunan gargajiya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano ya cashe gwamnoni:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel