Dino Melaye ya kushe gwamna Bello akan aikin wutan lantarki

Dino Melaye ya kushe gwamna Bello akan aikin wutan lantarki

-Dino Melaye ya sake sukan gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

- Gwamna Yahaya Bello ya samar ma jama’ar Kotu transforma a Lokoja

- Zamu mu cigaba da samar da wutan lantarki domin karfafa kananan masana’antu – Inji gwamna Bello

Senata mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalissan dattawa ta kasa Dino Melaye ya kushe bukin bude transformer mai karfin KVA 300 a garin Lokoja da gwamna Yahaya Bello ya kaddamar.

A takaitacen jawabin da gwamnan yayi wajen bukin, yace an samar da transforman ne bisa ga alkawuran da yayi ma jama’a wajen yakin neman zabe na samar da wutan lantarki domin karfafa kananan masana’antu na gida.

KU KARANTA KUMA: Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a ArewaRa’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Dino Melaye ya kushe gwamna Bello aikin wutan lantarki

Dino Melaye ya kushe gwamna Bello aikin wutan lantarki

Gwaman ya cigaba da cewa, za’a cigaba da fadada aikin samar da wutan lankarkin zuwa wasu sassan jihar domin taimaka ma masu sana’ar hannu sun bunkasa aikin su.

Gwamna Bello yayi kira da jama’a da su kulla da transforman kar bata gari su lalata shi kuma su dage wajen biyan kudin wuta a kan lokaci domin hukumar samar da wutar lantarkin da cigaba da samar masu da wutan lantarkin.

Shi kuma Senata Dino Melaye wanda a cikin kwanakin nan basu ga maciji da gwamna Bello, ya dauki hoton transforman yasa a shafinsa na facebook kuma yayi rubutu kamar haka:

“Ji yadda aka shirya babbar liyafa kawai domin gwamna Bello ya kadamar da transformer kwara daya a garin Koto tun hawan sa kan kujeran mulki, Allah dai ya isa!!!

Idan ba’a manta ba kwana kin baya NAIJ.COM ta bada rahoton baddakallar da ke tsakanin Dino Melaye da gwamna Yahaya Bello inda Dino ke zargin gwamna Bello da hannu wajen kiranye da jama’ar mazabar sa suke yunkurin masa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel