Kiranye: Dino Melaye ya garzaya kotu

Kiranye: Dino Melaye ya garzaya kotu

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce ta samu korafi daga al’umman mazabar yammacin Kogi, na shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye

- Tuni dai hukumar ta sanya rana domin tantance sa hannun Jama’ar da ke bukatar yi wa Sanatan kiranye domin daukar mataki na gaba

- Sanatan ya garzaya kotu domin a dakatar da yunkurin maida shi gida

Rahotanni sun kawo cewa a makon da ya gabata ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta ce ta samu korafi daga al’umman mazabar yammacin Kogi, na shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye.

Tuni dai hukumar ta sanya rana domin tantance sa hannun Jama’ar da ke bukatar yi wa Sanatan kiranye domin daukar mataki na gaba da dace.

KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Darajar Dalar Amurka a lokacin Idi

Kiranye: Dino Melaye ya garzaya kotu

Kiranye: Dino Melaye ya garzaya kotu

Bisa ga rahoto tuni dai Sanatan ya garzaya kotu domin a dakatar da yunkurin maida shi gida, sai dai hukumar zaben ta ce ba ta da masaniya a kan maganar kotu, kuma babu abin da zai hana ta aiwatar da wannan aiki a halin yanzu.

Kwamishinan hukumar zabe na Arewa ta tsakiya Mohammed Haruna, ya ce kwanan nan za’a fara shirin kada kuri’ar raba gardama, da zarar an kammala tantance sa-hannun al’ummar mazabar Sanatan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel