Korar Kabilar ibo: Zan amsa kiran hukuma idan sun neme ni - Inji Yerima

Korar Kabilar ibo: Zan amsa kiran hukuma idan sun neme ni - Inji Yerima

- Daya daga cikin shugabanin kungiyoyin matasan arewa yace a shirye yake ya amsa kirar hukuma idan sun neme shi.

- Duk mai son kirkiran sabuwar kasa yakoma garin su ya kirkiri kasar – inji Yerima

- Ban aikata wani laifi ba, na fadi ra’ayi na ne kamar yadda dokar kasa ta bani dama – inji Yerima

Shugaban wata daga cikin kungiyoyin samarin arewa wato (Arewa youths consultative forum) mai suna Shettima Yerima ya shaida ma manema labarai a ranar talata cewa a shirye yake da amsa gayyatar jami’an tsaro don amsa tambayoyi idan sun neme shi.

Ya cigaba da cewa, ba wani dalili da zai sa ya gudu ko ya buya don bai aikita wani laifi, kawai dai ya fadi ra’ayinsa ne a matsayinsa na dan Najeriya kamar yadda dokar kasar ta baiwa kowa daman fadin ra’ayin nasa.

Yayi wannan maganan ne a lokacin da manema labarai ke hira dashi kuma suka tambaye shi akan rade-radin da akeyi na cewa ya gudu zuwa kasar Chadi.

KU KARANTA KUMA: Ra’ayin Dangote game da wa’adin da aka baiwa Inyamurai a Arewa

Korar Kabilar ibo: Zan amsa kiran hukuma idan sun neme ni - Inji Yerima

Yarima ya ce zai amsa kiran hukuma idan sun neme shi

Bayan Yeriman wasu samarin da suka goyi bayan yunkurin korar kabilar ibon sun hada da Nastura Sherif na kungiyar (Arewa citizen’s action for change); Aminu Adam na kungiyar (Arewa youth development foundation); Alfred Solomin na kungiyar (Arewa students forum); Abdul-azeez Suleiman na kungiyar (Northern Emancipation Network); da kuma Joshua Viashman na kungiyar (Northern Youth Vanguard)

A wata hirar da Shettima Yerima yayi da yan jarida, ya ce:

Ban boye ba kuma bana shirin boyewa, ya kamata mu fadi magana a yadda take. A halin yanzu babu wanda yake nema na kuma idan an neme ni a shirye nake in amsa kirar. Ba wasa nakeyi ba. Babu wanda ke nema na kuma ba buya nakeyi ba, ni dan Najeriya ne kuma yanzu haka ina kauyen mu. Idan an neme ni zan amsa kiran domin ban fi karfin doka ba."

Ya cigaba da cewa: “Wane dalili zai sa in boye? An san suna na kuma an san fuska ta.

“Babu wani dalilin da zai sa in boye don banyi laifi ba. Mutane ne sukace suna son su tafi, ni kuma nace suyi ta tafiyar, menene laifi a cikin wannan.

“Ba yadda zaka zauna a kasar mu kuma kace kana son kirkirar wata kasar daban, idan kana son kirkirar sabuwar kasa toh ka tafi garinku can ka kirkiri kasar. Ba dai a garin mu, illa iyaka. Magana ce mai sauki, ni banyi wani laifi ba."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel