Za mu ci gaba da goyon bayan Najeriya kan Boko Haram – Inji MDD

Za mu ci gaba da goyon bayan Najeriya kan Boko Haram – Inji MDD

- MDD ta nanata goyon bayan ta ga gwamnatin Najeriya kan Boko Haram

- Guterres ya yi Allah wadai da jerin hare-haren kunar bakin wake na baya bayan nan a Maiduguri

- Sakataren ya taya wadanda suka ji rauni a cikin jerin hare-haren samu lafiya

Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Antonio Guterres, ya nanata da cewa kungiyar ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin tarayyar Najeriya kan yadda za a durkushe kungiyar Boko Haram da kuma ta'addanci.

A cikin wata sanarwar da kakakin sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric ya fitar, Guterres ya yi Allah wadai da jerin hare-haren kunar bakin wake a Maiduguri a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.

NAIJ.com ta ruwaito cewa sakataren ya mika ta'aziyya ga mutanen jihar da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya domin asarar rayuka da aka yi.

Za mu ci gaba da goyon bayan Najeriya kan Boko Haram – Inji MDD

Kungiyar Boko Haram

KU KARANTA: Ba za’a kulle Jami’ar Maiduguri ba duk da hare-haren Boko Haram – Shugaban UNIMAID

Shugaban na MDD ya kuma taya wadanda suka ji rauni a cikin jerin hare-haren kunar bakin wake samu lafiya.

A cewar shi, yana fatan cewa, wadanda ke da alhakin wannan harin za a hanzarta kawo adalci a kansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel