Sauya fasalin Najeriya kadai ba zai warware matsalolin ta ba – Inji wani tsohon minista

Sauya fasalin Najeriya kadai ba zai warware matsalolin ta ba – Inji wani tsohon minista

- Cif Don Etiebet ya ce sauya fasalin Najeriya kadai ba zai warware matsalolin ta ba

- Etiebet ya ce a yanzu haka abin da kasar ke bukatar shine kyakyawar tsarin gwamnati

- Tsohon ministan ya ce dole ne kasar ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa

Tsohon ministan man fetur, Cif Don Etiebet, ya ce sauya fasalin kasar kadai ba zai warware matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu halka ba.

Ya ce: " Abin da Najeriya na bukatar yanzu haka gaskiya shine kyakyawar tsarin gwamnati".

"Ina ganin ya kamata ‘yan Najeriya su yi godiya ga gwamnonin jam’iyyar APC wato APC’s Governors Forum wandanda suka fito don nuna goyi bayan su ga wannan tsari wanda zai magance kalubale da kasar ke ciki da kuma hadin kai Najeriya”.

Sauya fasalin Najeriya kadai ba zai warware matsalolin ta ba – Inji wani tsohon minista

Tsohon ministan man fetur, Cif Don Etiebeth a lokacin da ziyarci fadar shugaban kasa da ke Abuja

NAIJ.com ta ruwaito cewa, tsohon ministan ya ci gaba da cewa, ya ce, a daidai wannan lokaci, dole ne mu ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa kuma a nemi hanyoyin da za a magance cin hanci da rashawa a duk fadin kasar gaba daya.

KU KARANTA: Ministar kudi na kasa ta wanke kan daga wani zargi

Za a iya tuna cewa a sakonsa da ya fitar na bikin karamar salla tsohon shugaban Najeriya a lokacin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bi sahun masu kiran da a sake wa kasar Najeriya fasali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi hakan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel