Karatu sai wane-da-wane: Jami’o’i fiye da 30 sun kara kudin makaranta

Karatu sai wane-da-wane: Jami’o’i fiye da 30 sun kara kudin makaranta

– Jami’o’i da dama sun kara kudin makaranta a Najeriya

– Wani Shugaban Kungiyar ASUU ya bayyana haka

– Malaman Jami’ar sun fadi dalilin kara kudin

Yanzu dai Talaka sai kara shan wahala kafin yayi karatu a Jami’a. Akalla Jami’o’in Tarayya 38 ne su ka kara kudin makaranta. Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU tace dole ce ta sa hakan.

Karatu sai wane-da-wane: Jami’o’i fiye da 30 sun kara kudin makaranta

Jami’o’i da dama sun kara kudin makaranta

Yanzu haka karatu a Jami’a zai zama sai wane da wane bayan da akalla akalla Jami’o’in Tarayya 38 su ka kara kudin makaranta a wannan makon. Shugaban Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na Jami’ar Ibadan Dr. Deji Omole ya bayyana haka.

KU KARANTA: Gwamna Wike ya kai wa Sultan ziyara

Karatu sai wane-da-wane: Jami’o’i fiye da 30 sun kara kudin makaranta

Dole ta sa Jami’o’i 38 sun kara kudin makaranta

Dr. Omole yace Gwamnatin Buhari tayi watsi da harkar ilmi a kasar wanda ya sa dole su ka dauki matakin kara kudin makarantun. Omole yace ba a Makarantun Gwamnati muhimmaci ba don na yaran Talakawa ne.

Irin su Jami’ar fasaha ta Akure sun daga kudin na su daga N13, 560 zuwa N83, 940. Sauran Jami’o’i irin su Ahmadu Bello ta Zariya da Bayero da ke Kano dai duk ba a bar su a baya ba inda za a rika biyan sama da N40, 000 a yanzu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me ya dace ayi wa Evans? [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel