Toh fa, Cinko: Wani gadan da China ta gina ta rushe bayan sati 2 da budewa

Toh fa, Cinko: Wani gadan da China ta gina ta rushe bayan sati 2 da budewa

- Gadan da wani kamfanin kasar China ta gina ta rushe gaba daya

- Gadan ta rushe makonni biyu bayan da shugaban kasar ya ziyarci aikin gadan

- Har yanzu ba a san dalilin rushewar gadan ba

Wani gada da kamfanin kasar China wato Chinese Overseas Construction and Engineering Company ta gina wanda aka kashe dallar Amurka miliyan 12 ta rushe gaba daya.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar wannan gadan dai ta rushe ne makonni biyu bayan da shugaban kasar ya ziyarci aikin gadan.

An kaddamar da gina wannan gadan bayan wata mumunar hatsari da ya faru a ranar 30 ga watan Agusta, 2014, a lokacin da mutane 11 suka hallaka bayan wani jirgin ruwan da suka hau ya kife, inda ta hallaka duka mutanen da ke cikin jirgin ruwan , yayin da suke yunkurin haye kogin. A cewar jaridar Afirka Review.

Toh fa, Cinko: Wani gadan da China ta gina ta rushe bayan sati 2 da budewa

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta

Wannan gadan da ake gina a kasar Kenya a mazabar Kenya Budalang'i wanda ke kusa da kan iyaka da kasar Uganda ta rushe a mako biyu bayan shugaban kasar Uhuru Kenyatta ziyarci duba aikin gadan.

KU KARANTA: Adadin Mutanen dake amfani da Facebook sun fi ýan ƙasar China yawa

Ba a san sabilin rushewar gadan ba tukuna, amma ana zargin cewa an yi gadan ne cikin hanzari gaba da ziyarar shugaban kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel