Jirgin shugaba Buhari dake ajiye a ingila yana hadiye fam dubu hudu a kullum

Jirgin shugaba Buhari dake ajiye a ingila yana hadiye fam dubu hudu a kullum

- Ana kashewa jirgin Buhari fam dubu hudu a kullum

- Zai fi dacewa a dawo da jirgin gida Najeriya har sai an sallame Shugaba Buhari

- Ana almubazaranci da kudin Najeriya a Ingila

Jirgin shugaba Buhari wanda ke ajiye a kasar ingila dai ana yana hadiye fam dubu hudu ne a kullum a matsayin kudin ajiya kamar yadda wata majiya ta bayyana. Duk da jirgin baya tsinana aikin komai a yanzu haka.

Karfe sha biyun daren yau zai cika kwana hamsin (50) kenan da jirgin ke zaman dirshan a wajen ajiyan kuma inda aka lisafa fam dubu hudu so hamsin zamu samu jimlan kudi naira miliyan tamanin (N80,000,000.000). idan mukayi la’akari da cewa fam daya yana daidai ne da N400.

Jirgin shugaba Buhari yana hadiye fam dubu hudu a kullum

Jirgin shugaba Buhari yana hadiye fam dubu hudu a kullum

Wannan dai babban kuskure ne ajiyar jirgin kuma ana kasha masa kudi mai dumbin yawa a yayin da mutanen Najeriya na fama da talauci a gida.

Abin da yafi dacewa shine a dawo da jirgin gida Najeriya, daga bisani idan shugaban likitoci sun sallami shugaba Buhari sai jirgin ya koma kasar ingila domin ya dauko shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel