Mutanen Jonathan sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

Mutanen Jonathan sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

– Mutanen Neja-Delta sun yi kaca-kaca da Nnamdi Kanu

– Nnamdi Kanu ya soki mulkin Shugaba Jonathan

– ‘Yan Kungiyar OBYC sun ja masa kunne kwanan nan

Matasan Ogbia na Yankin Neja-Delta sun soki Nnamdi Kanu. Hakan ya zo bayan Kanu ya soki tsarin mulkin Jonathan. Nnamdi Kanu yace Jonathan bai tsinana komai ba a lokacin sa.

Mutanen Jonathan sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

Jagoran tafiyar Biyafara Nnamdi Kanu

‘Yan Kungiyar Matasan Ogbia na OBYC da ke Yankin Neja-Delta sun soki jagoran IPOB Nnamdi Kanu game da sukar mulkin Jonathan. Nnamdi Kanu yace Jonathan bai tsinana komai ba lokacin da yayi mulki.

KU KARANTA: Gwamnan PDP ya ce ba ruwan sa da Biyafara

Mutanen Jonathan sun yi kaca-kaca da Jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

‘Yan Neja-Delta sun ja kunnen Nnamdi Kanu

Mutanen Neja-Delta sun yi tir da Kanu inda su ka gargade sa da yi wa tsohon Shugaba Jonathan rashin kunya. ‘Yan Kungiyar su kace Jonathan Dattijon arziki ne don haka Kanu ya guji kawo tsohon Shugaban cikin hayaniyar sa ta Biyafara maras kan gado.

Kun san cewa a jiya Gwamna Nyesom Wike ya kai wa Sarkin Musulmi ziyara. Nyesom Wike dai yace ba ya goyon bayan a kirkiro wata kasar Biyafara inda ya nemi a hada kai a Kasar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnmadi Kanu yayi jawabi ga Jama'a a Kudancin kasar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel