Wani mutum ya yi musayar yaron da ya sata da buhun shinkafa 3

Wani mutum ya yi musayar yaron da ya sata da buhun shinkafa 3

A wani lamari mai kama da almara, wani mutumi ya saci yaro dan shekara 10 a kan titi ya yi musayar sa da buhun shinkafa 3 a wani shagon sayar da kayan masarufi a yankin Ijegun dake jihar Lagas.

Rahotanni sun kawo cewa mutumin ya samu yaron ne a kan hanyar sa ta zuwa sayo wa mahaifiyar shi man gyada, inda ya yaudareshi da cewar shi dan uwan mahaifiyar ne har ma ya raka shi sayen man gyadan.

Daga baya, mutumin wanda bai bayyana sunan shi ba, ya dauki yaron zuwa wani shagon da ake sayar da buhuhunan shinkafa, ya nuna cewa tare suke da yaron, wanda ya kira kanin shi.

Yarinya mai jiran shagon mai suna Deborah ta fadawa Jaridar Vanguard yadda Mutumin ya karbi buhuhunan shinkafa guda 3 ya bar yaron a gurin ta da zummar zai je ya dawo da kudaden.

KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Darajar Dalar Amurka a lokacin Idi

Ta ce ta yi jiran duniya ba ta ga mutumi ba har na tsahon awa daya wanda a lokacin ne ta bukaci yaron ya kaita wajen mahaifiyar shi.

Yaro kuwa ya ce mahaifiyar shi ba ita ya saye shinkafa ba, hasali ma a kan titi ya hadu da wannan mutumi.

A bangare guda kuwa iyayen yaro sun shiga rudani bayan da suka yi ta jiran yaron ya dawo daga aike ba su gan shi ba kuma tuni suka bazama nema.

Lamarin ya tabarbare da suka je shagon da ake sayar da man gyadan aka fada masu cewa an ga yaron tare da wani mutum.

Lamarin dai yanzu haka yana wajen ‘yan sanda.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da ‘yan sanda sun baiwa iyayen yaron dan su, masu shagon sun tire akan sai an biya su kudaden shinkafar su.

Yanzu haka dai ‘yan sanda na kan neman mutumin yayin da suke yunkurin sasanta masu shago da iyayen yaron.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel